Tuwita
Fesbuk
Gogul
Yutob
Rss

Rashin jirkitar Alkur'ani mai tsarki

Rashin jirkitar Alkur'ani mai tsarki
 • fassarar Hassan Adamu
 • 2016-03-06 19:03
 • Fitarwa
 • PDF
 • Shiga Ta Hanyar Fesbuk
 • Shiga Ta Hanyar Tuwita
 • Shiga Ta Hanyar Gogul
 • Shiga Ta Hanyar Was'of
 • Adadin BaƘi 3392
 • Adadin Ra'ayoyi 0
 • -
  +

RASHIN JIRKITAR ALQUR'ANI MAI TSARKI


Duk da yada batanci da munanan kalamu da akeyi dangane da Shi'a, Mu munyi imani cewa wannan alqur'anin da yake a hannun mu da kuma hannun sauran musulmai, shine ainihin Alqur'anin da aka saukarwa da Annabin Rahma Muhammad dan Abdullah (SAWA) kuma hatta kalma daya bata qaru ko ragu ba.


     A littattafa da dama da muke dasu a Tafsiri, Usul al-Fiqhu da wasun su, an rubuta wannan bahasin a fadade tare da dalilai na hankali, nassi da ruwayoyi mun tabbatar da wannan.


     Mu tare da dukkan malaman musulunci wadanda suka hada da Shi'a da ahlus Sunna mun hadu akan cewa babu abin da ya qaru a cikin Alqur'ani, sannan kuma mafi yawa daga cikin malamai manazarta masu binciken ilmi na dukkan bangarorin biyu sun hadu akan cewa babu abin da ya ragu (naqasu ko rashin cika) daga Alqur'ani.


Wasu tsirari daga dukkan bangarorin biyu, sun tafi akan ragi (rashin cikar) wani abu daga Alqur'ani wadda maganganun su basu sami karbuwa ba a tsakanin dukkan fitattun malaman musulunci.


LITTATTAFAI BIYU DAGA DUKKAN BANGARORIN (SHI'A DA SUNNA)


Daga kalaman su Ibnil Kadib wani dan Misra wanda yake ahlus sunna ne wanda ya rubuta littafin «الفرقان فى تحريف القرآن» wanda aka yada shi a shekarar 1948 A.D. (1367 A.H.) wadda a yayin da Jami'ar Al'azhar ta farga da abin da littafin ya qunsa sai ta tattara littafin daga duk gurin da zata iya sai ta batar dashi, amma ba a rasa 'yan tsirari da suka fada hannun mutane nan da can.


Hakazalika littafin «فصل الخطاب فى تحريف كتاب رب الأرباب» wanda wani daga cikin masana hadisi 'yan shi'a (muhaddisin) mai suna Haji Nuri ya rubuta, wadda aka buga shi a shekarar 1291 A.H. kuma da buga shi ya fuskanci suka daga manyan malaman Hawzar Najaf mai tsarki, nan da nan aka bayar da umarnin tattara shi, kuma an rubuta littattafai da dama da suke yin Raddi akai, daga cikin manyan magabata da suka yiwa littafin faslul khidab raddi sune;


Fitaccen malami marigayi Sheikh Mahmud bin Abil qasim, wanda aka fi sani da Mu'arrab Tahrani wanda ya rasu a shekara ta 1313 wadda littafin da ya rubuta shine, «كشف الإرتياب فى عدم تحريف الكتاب». Marigayi Allama Sayyid Muhammad Husain Shahristani wanda ya rasu a shekara ta 1325 ya rubuta littafin raddi akan littafin Faslul khidab na Haji Nuri, mai suna, «حفظ الكتاب الشريف عن شبهة القول بالتحريف». Marigayi Allama Balaghi wanda ya rasu a shekara ta 1352, yana daga cikin manazartan Hawzar Najaf mai tsarki, a cikin aikin shi mashhuri wato littafin «تفسيرآلاء لارحمان» yayi fasali guda musamman da yake yin raddi akan Faslul khidab.[1] Mu ma a littafin «انوارالاصول» munyi bahasi budadden gaske dangane da rashin jirkitar Alqur'ani mai tsarki da kuma bayar da qwaqqwarar amsa ga shubhohin Faslul khidab.


Marigayi Ha'ji Nuri duk da shi malami ne amma kamar yadda Allama Balaghi yace, ya dogara ne da raunanan ruwayoyi wadda shi da kanshi bayan yaduwar littafin yayi nadama akan abin da yayi, kuma dukkan manyan malaman Hawzar ilmi ta Najaf mai tsarki sun kira wannan aiki daya daga cikin manyan kura-kuran shi bayyanannu.[2]


Wani abin jan hankali shine bayan yaduwar littafin Faslul khidab, Ha'ji Nuri ya fuskanci suka ta ko'ina, wadda hakan yasa dolenshi ya rubuta wata wasiqa ko maqala yana kare kanshi cewa yana nufin rashin jirkitar littafin Allah ne, da kuma cewa anyi mashi mummunar fahimta ne.[3]


Marigayi Allama Sayyid Habatuddin shahristani yana cewa: lokacin da nake a Samara, marigayi Mirzay shirazi babba ne ya mayar da can cibiyar ilmi da fannoni na shi'a, a duk lokacin da muke halartar majlisi, kafin fara karatu sai yayi kakkausar suka ga ha'ji Nuri da littafinshi da babbar murya, wasu ma da munanan kalamai suke kiran shi. [4]


Da duk wadannan yanzu ana ganin ya kyautatu a danganta ko a laqawa aqidar shi'a maganganun sheikh Nuri?


Yanzu wasu daga wahabiyawa masu ta'asubanci sun dauki wannan littafi na Faslul khidab suna fakewa dashi suna danganta aqidar jirkitar Alqur'ani ga 'yan shi'a, alhali cewa:


Idan duben littafi guda daya, ya zama dalili akan cewa wannan al'amari yana daga cikin aqidun shi'a, to ya zama wajibi suma malaman ahlus sunna mu danganta musu yarda da jirkitar Alqur'ani, saboda Ibnil Khadib Misri ma yayi littafin Alfurqanu fi tahrifil qur'an, kuma idan Allah wadai din da malaman Al'azhar suka yi da littafin nashi, ya wanke ahlus sunna, to Allah wadai, suka da raddin da malaman Najaf maitsarki suka yiwa Faslul khidab shima daliline akan haka ga shi'a (wato ya wadatar wajen wanke shi'a daga waccan zargi). A tafsirin Qurdabi da Durul'manthur dukkan su suna daga cikin fitattun littattafan tafsirin ahlus sunna, an naqalto daga A'isha (matar Annabi [SAWA]) tana cewa:


«انها - اى سورة الأحزاب – كانت مأتى آية فلم يبق منها إلا ثلاث و سبعين


za mu ci gaba daga nan insha Allah.


 


[1] آلاء الرحمان، جلد 1، صفحة 25.


[2] آلاء الرحمان، جلد 2، صفحة 311


[3] الذريعة، جلد 16، صفحة 231.


[4] Burhan rushan, shafi na 143 (wannan littafi ne na harshen farisanci

jirkita

Ra'ayoyin Masu Shigowa
Babu Haƙƙin Tasarrufi.
www.haditv.com | Powerd by : Dijlah