Tuwita
Fesbuk
Gogul
Yutob
Rss

Gajerun labarai masu dauke da darusa kashi na 2

Gajerun labarai masu dauke da darusa kashi na 2
 • Mr. Hassan Adamu
 • 2016-03-13 10:03
 • Fitarwa
 • PDF
 • Shiga Ta Hanyar Fesbuk
 • Shiga Ta Hanyar Tuwita
 • Shiga Ta Hanyar Gogul
 • Shiga Ta Hanyar Was'of
 • Adadin BaƘi 4443
 • Adadin Ra'ayoyi 0
 • -
  +

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM


ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALI MUHAMMAD


 


MACE MAI KAMAR MAZA


Ummu salim matar Abu Dalha ansari, ta kasance daga cikin mata madaukaka na Bani hashim. lokacin da abu dalha ya nemi aurenta, sai tace dashi: ta wata fuskar kai mutun ne da ka cancanci a aura, amma saidai kash! kai ba musulmi bane, ni kuma musulma ce, dan haka idan zaka musulunta, na yarje maka da musuluntar ka ya zama a matsayin sadaki na. Bayan musuluntar Abu dalha, ya kasance daga cikin manyan sahabban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa alihi wa sallam). A yaqin Uhud ya kasance cikin wadanda suka tsaya dan kare ma'aikin Allah, idan aka yo harbi yana tura qirjinshi gaban Ma'aikin Allah, yana cewa: kafin harbi ya isa ga Manzan Allah, to ya fara fasa qirjina tukun.


Abu dalha ya kasance yana da wani Da (yaro) da yake matuqar son shi qwarai. sai wata rana yaron ya kamu da rashin lafiya. Ummu salim wacce tana daga cikin madaukakan matan musulmi, da ta lura cewa kamar cutar yaron su ta ajali ce, sai kawai ta qirqiri wani saqo, ta baiwa mijinta (Abu dalha) ya kaiwa Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa alihi), bayan fitarshi zuwa wajen aiken, sai Allah yayiwa yaron cikawa (mutuwa). sai Ummu salim ta rufeshi da mayafi ta dauke shi ta kai shi can qarshen kusurwar daki ta ajiyeshi, sannan tayi sauri ta dora abinci, ya dahu ta sauke, sai kuma ta shiga wanka, ta fito tayi ado, ta yadda zata ja hankalin mijinta.


Da abu dalha ya dawo daga gurin ma'aikin Allah, sai ya tambayi halin (jikin) yaro, tace mashi yana can a kwance. sai ya buqaci abinci, tayi sauri ta kawo suka zauna suka ci tare, bayan cin abinci kuma TA GABATAR MASHI DA KANTA GARESHI, bayan ya nutsu sai Ummu salim tace: a 'yan wasu lukuta akwai amana a hannu na, amma yau na mayarwa da mai ita (amana), da fatan ba zaka damu da hakan ba?. sai Abu dalha yace: meye na damuwa dan kin sauke nauyin da ya hau kanki!. sai ummu salim tace: Dama abin da nake so in sanar da kai shine, Dan (yaron) ka, amanar Allah ce a hannun ka, to yau mai abu ya karbi amanar Shi. Sai abu dalha cikin dakiya da nutsuwa, yace: Nine ya kamata in sami wannan dakiya (Istiqama) fiye da ke mahaifiyar wannan yaro, dan haka babu bata lokaci sai ya tashi yaje yayi wanka, sannan yazo yayi salla Raka'a biyu. sai ya tafi gurin ma'aikin Allah ya bashi labarin mutuwar Danshi, sannan ya gaya mashi irin aikin da ummu salim tayi (wato halayen da ta nuna na juriya da dakiya da kwantar da hankalin mijinta).


 


Sai Manzan Allah (sallallahu alaihi wa alihi) yace: Allah Ya sada ku da albarkar wannan rana, sannan kuma yace: Godiya ta tabbata ga Allah da nima ya azurta al'umma ta da Mata irin Sa'biratu Bani Isra'ila (wata mata ce mumina a al'ummar bani isra'ila).


 


MAFI GIRMAN HAQURI; SHINE KADA MUYI SABO: An taba yin wani bawan Allah mai matuqar yawaita bauta a al'ummar da ta gabata lokaci mai tsawo. Wanda bai taba ruduwa da rudun duniya ba. Hakan sai ya sa Ran babban shaidan (Iblis) ya baci matuqa. Sai babban shaidan (Iblis) yayi kuwwa mai qarfi, sai ya tattara dakarunsa, duk suka taru a kewaye dashi. sai ya tambaye su kamar haka: Waye a cikin ku zai iya batar da wancan A'bid (mai yawan bauta) din? sai daya daga cikin su yace, zan iya. Iblis yace, ta yaya? sai yace, ta hanyar Mata, Iblis yace, hakan ba zai yi tasiri gare shi ba, saboda ya kasance kwata-kwata bashi da alaqa dasu kuma bai San su ba. sai wani shaidanin ya tashi yace, ni zan batar dashi da Giya, shaye-shaye da sauransu. Iblis yace, kaima baza ka iya yaudararshi ba ta wannan hanyar.


Sai shaidani na uku ya tashi yayi iqrarin batar dashi ta hanyar fakewa (pretending) da da bayyana a matsayin mutumin kirki mai yawan bautar Allah. Sai Iblis yace, lallai kai za kayi nasara akanshi. Sai shaidanin nan ya shiga gurin mai bautar nan a matsayin mutumin kirki, yaje kusa da yadda mutumin yake yin ibada, shima ya tashi sallah.


 


Mai ibadar nan bayan wasu 'yan lokuta yayi sallah da yawa, sai ya tsaya domin ya huta, amma shaidanin nan ko gezau (wato ba sassauci). ganin haka sai mai ibadar nan, ya fara jin qasqanci ganin ga Sabon zuwa, Amma ya kere masa sa'a. cikin tawali'u (qasqan da kai da girmamawa) sai ya tambayi shaidanin cewa, kai kuwa ya akayi ka samu kuzari da tsayuwa wajen bautar Allah haka, babu ko gajiya? Amma la'anannen bai ko Kula shi ba, kawai ya ci gaba da yin sallah, ya dai takura shi da tambaya makamancin haka, cewa meye ya kaishi ga wannan babban matsayi?. Sai shaidanin nan yace, Kai bawan Allah! na kasance nayi SABO, Amma sai na tuba, kuma kodayaushe ina sanya Sabon nan a raina. wannan ne ya bani qarfin yin ibada ba tare da gajiya ba. Sai mai ibadar nan ya tambaye shi cewa, wanne sabo ne, nima in samu in aikatashi. Sai shaidan yace masa kaje gari kaza... ka shiga gidan wata mata mai zaman kanta, sai ka bata Dirhami biyu. sai mai ibadar nan yace ai ko Dirhami biyun bani da, sai shaidan ya dauko daga gurin da yake zaune, ya miqa mashi.


Sai mai ibadar nan ya qudiri azama, ya nufi waccan gari, cikin kayan Shi na kamala, da ya isa garin, sai ya tambayi gidan matar nan mai zaman kanta, koda mutane suka ga mutun cikin kamala yana tambayar wancan gida, sai suka dauka cewa, zai je ya shiryar da matar ne, sai suka nuna masa. Da shigar shi gidan sai ya jefa mata dirhamin nan biyu, yace ki tashi mu shiga daki. sai ta tashi suka tafi dakin ta, tace dashi, ya kai wannan bawan Allah, kazo min a wani irin yanayin da babu wanda ya taba zo min a irin shi (wato yanayi na kamala). Dan haka Dan Allah zan so ka gaya min, me yasa ka zabi kazo gurina? sai ya gaya mata duk abin da ya faru. Sai tace dashi, Ya kai bawan Allah, ka sani Qin aikata zunubi yafi sauqi akan tuba bayan an aikata shi. ka sani ba zai yiwu ba mutun yayi zunubi yana sane daga baya ya tuba, sannan kuma kace zai sami babban matsayi a gurin Allah kamar yadda kake sawwarawa. Dan haka lallai kowaye Wanda ya turo ka dinnan, to shaidan ne yayi badda kama ya zo maka domin ya batar da kai. ka koma inda ka fito ba zaka iske Shi ba acan. sai mai ibadar nan ya koma gida.


 


Wannan Mata kuma sai Allah Ya karbi ranta a wannan daren. kashegari da safe kuma sai mutanen garin suka ga rubutu a qofar gidan nata an rubuta cewa: dukkan mutanen garin su halarci Jana'izar wannan Mata, saboda tana cikin wadanda zasu shiga aljanna. sai mutane suka yi mamaki, Dan,haka sai basu yi hakan ba, suka bar ta har tsawon kwana uku. sai Allah Yayiwa annabin wannan zamanin wahayin dukkan abin da ya faru, mai ruwayar yace, Annabi Musa Alaihissalam ne. Allah Yace dashi kaje ka sallaci Mata wance saboda na gafarta Mata. na tanadar Mata aljanna saboda cetar bawa Na da tayi daga Saba min.


 


KYAKKYAWAN QARSHE NA GA MASU TSORON ALLAH: An taba yin wani mumini a zamanin da, da ya kasance yana yawaita fadar: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki; kuma Kyakkyawan qarshe na ga masu tsoron Allah." to ashe wannan furuci yana qona Ran Iblis (babban shaidan). Dan haka sai ya turo daya daga cikin yaranshi a sifar mutun domin yazo ya canzawa muminin nan tunaninshi akan wancan furuci da yake yi. koda qaramin shaidanin yazo, da yaji muminin nan ya kuma fadar maganar hikimar da ya saba, sai shaidanin yace dashi "kai malam kyakkyawan qarshe yana ga masu kudi da dukiya." sai muminin nan yace a'a ba haka bane, lallai kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, shaidanin nan yayi iya yinshi domin ya canza muminin nan, amma ya kasa. Sai yace to, mu nemi wani mutumin a hanya ya raba mana gardama, kuma da sharadin cewa, duk wanda akayi galaba akanshi to za a yanke hannun shi daya. Mumini ya yarda, sai ga wani mutumi yazo wucewa, suka tambaye shi, sai yace musu, "kyakkyawan qarshe na ga masu kudi da dukiya'. Shikenan sai aka yanke hannun mumini guda daya, sai shaidan yace dashi ka gani ko? na gaya maka ai! sai muminin nan yace ai lallai shi har yanzu bai yarda ba, sai shaidanin ya kuma cewa, to mu tambayi wani mutun din da zai sake bullowa, shima wannan karon za a cire hannun duk wanda akayi galaba akanshi. Mumini ya yarda. sai ga wani mutun ya bullo, aka tambayeshi, shima ya bada amsa kamar na farko, sai aka cire daya hannun muminin. shaidanin ya kuma ce mashi, ka gani gashinan ka rasa hannaye biyu, na gaya maka, abin da kake cewa ba haka bane. Muminin nan ya kuma cewa, ina! ai lallai kam, kyakkyawan qarshe na ga masu tsoron Allah, sai shaidanin yace, to a kuma tambayar mutun na uku, amma a wannan karon, Kai za a cirewa duk wanda akayi galaba akanshi, Mumini ya yarda, sai Allah Ya turo mala'ika a sifar mutun ya biyo hanyar, sai suka fara haduwa dashi, suka tambaye Shi, sai ya dauki hannun muminin nan daya ya dora Shi a gurin da yake, Sannan ya Shafi gurin, sai hannu ya koma yadda yake, ya dauki dayan ma yayi masa kamar na farko. Sannan sai ya fille kan shaidanin nan, yace "LALLAI KYAKKYAWAN QARSHE NA GA MASU TSORON ALLAH". 


TAMBAYOYI HUDU: Wani mutun yazo gurin Imam Ali (Alaihissalam) yace: Ba na tambaye ka abubuwa hudu ba, ka bani amsar su?


1. Menene wajibi? kuma meye yafi zama wajibi?


2. Menene Kusa (kusanci)? kuma meye mafi Kusa?


3. Menene abin al'ajabi (mamaki)? kuma meye mafi al'ajabi?


4. Mecece wahala? kuma meye tsananin wahala? Sai Imam


Ali (Alaihissalam) yace: ...


1. Wajibi shine yiwa Allah Ta'ala Biyayya (Da'a). Amma mafi zama wajibi shine, barin Sa6o.


2. Kusa itace Ranar Alqiyama. Amma mafi kusanci itace Mutuwa.


3. Abin Al'ajabi kuwa itace Duniya. Amma mafi zama abin al'ajabi shine Son Duniya.


4. Wahala kuwa shine Kabari. Saidai mafi wahala shine Zuwa babu guziri.


Allah Ta'ala Yayi mana kyakkyawan Qarshe.


 


LAILA DA MAJNUN: An taba yin wani mutumi wai Majnun, ma'ana Wanda Hankalin Shi ya gushe. Tambaya!!! garin yaya ya Sami wannan suna? Da farko dai wannan mutumi, kawai ya ji sunan Laila ya bugi kunnenshi, sai kawai ya rika sawwarata a zuciyarshi, har ya kamu da sonta, wadda Soyayyar tata har takai wani yanayi da ba zai iya haqura ba, ba tare da ya nemi abin son nan tashi ba. Dan haka sai ya quduri aniyar fita neman abin sonshi.


Ya fita yaje wannan gari, yaje waccan gari, amma babu labarin Laila, haka yayi ta Shan wahala da qetara garuruwa domin haduwa da abin sonshi. a qarshe dai ya hadu da wani da ya taba jin labarin Laila, sai yake ce mashi tana qasa kaza da kaza... dai yayi masa kwatancen qasar da nisa daga yadda yake, haka dai Majnun ya qara daura damarar tafiya. -kamar yadda kowa ya sani cewa ance Garin masoyi baya nisa, kuma so yana gusar da duk wata wahala daga Ido ko Rai na masoyi- Dan haka sai Majnun yaci gaba. To!!! Yau dai Allah Yayi ga Majnun a gari kuma a qofar gidan da Laila take!!! To bamu San me zai faru ba!!! masu biye damu ku sani fa mun tsallake wasu wahalhalu da hatsarurruka da bala'o'in da Majnun ya gamu dasu a hanya domin zuwa gurin abin Sonshi. To amma koda Majnun ya qwanqwasa qofar Laila, sai Laila ta tambaya, Wanene? sai Majnun yace mata "Nine Majnun" sai Laila tace dashi "Je ka ba zan bude maka ba." sai Majnun ya ja da baya ya koma, sai ya sami qarqashin wata bishiya ya zauna, zuwa wani dan lokaci wutar so ta kuma ruruwa a zuciyarshi, sai ya tashi ya koma bakin qofar Laila, ya kuma qwanqwasawa, tazo bakin qofa tace Wanene? a wannan karo, sai yace da ita "KE CE!!!" -Allahu Akbar, kunji fa masu saurare, wato duk son da yake yi mata a baya, tunda ya iya shaida kanshi da yace mata "Nine Majnun' a qwanqwasawar farko, hakan yana nufin ba Majnun din bane, saboda mahaukaci na Haqiqa baya iya shaida kanshi, amma da ya koma gefe bayan taqi bude mashi, a yayin da Mahaukacin So din ya taso masa, sai ya gaza bambancewa tsakanin Kanshi da abin Sonshi- kar in cika ku da surutu, da yace mata KECE ai sai ta bude mashi Qofa. da bude qofa, sai ga Laila ta bayyana ga Majnun. sai ga Laila ta bayyana Tsohuwa, Ajuza, Rarrauna. Sai take cewa Majnun: "TO KA GANNI DAI YADDA NAKE, TSOHUWA, RARRAUNA, NA GAJI. DAN HAKA DA ZAKA MAYAR DA SON KA GA WANDA BAYA TSUFA, BAYA GAJIYA, WANDA YA MALLAKEKA, YA MALLAKENI? TO DA KA DANDANA ZAQIN SO."


TA'AZIYA: Salamu alaikum 'yan uwa masu biye da wannan zaure. wannan Aji yana yi muku Ta'aziyya da gaisuwa na juyayin shahadar 'Uwar sharifai Sayyida Zahra Salamullahi Alaiha'. kuma wannan Aji yana mai kira da tuni ga 'yan uwa da su qara duba rayuwar wannan baiwar Allah Mazluma, domin koyi da kyawawan halayenta da suka hada da Dakewa da rashin tsoro wajen bayar da kariya ga saqon Allah da kuma Shi Wanda yazo da saqon wato ma'aikin Allah Sallallahu Alaihi wa Alihi. ta kasance akan wannan gwagwarmaya tun lokacin mahaifin nata yana wannan Duniya, zamu iya ganin yadda tayi gwagwarmaya da mushrikai kamar irin su Abu jahl d.s. haka kuma ta wanzu tanayi bayan mahaifinta ya bar wannan duniyar. Hakazalika akwai koyarwar kyautatawa Dan Adam daga rayuwar wannan baiwar Allah mazluma, ta yadda zamu ga yadda ta rika kyautatawa maqwabta da raunana.


Akwai lokacin da mabuqaci ya qwanqwasa qofar gidanta, dan neman abin da zai ci, a daidai lokacin bata da kudi ko abincin da zata bashi, kawai sai dauko abin wuyan ta mai qima ta bashi, yaje ya sayar domin ya biya buqatarshi... wannan kenan dama wasu da ba zasu qirguba... haka hatta wajen manajati da Allah, a qarshen munajati ta kan fara da yiwa maqwafta addua, sannan iyalinta. daga cikin mashhurin maganarta takance dangane da alkhairi: "Maqwafta Sannan gida." Allah Ya bamu qwarin gwiwar koyi da wannan Baiwa taShi Tsarkakakka.


 

Ummu salim Jaruma Ranar shahada

Ra'ayoyin Masu Shigowa
Babu Haƙƙin Tasarrufi.
www.haditv.com | Powerd by : Dijlah