Tuwita
Fesbuk
Gogul
Yutob
Rss

QARYA

QARYA
 • Mr. Hassan Adamu
 • 2016-05-20 10:05
 • Fitarwa
 • PDF
 • Shiga Ta Hanyar Fesbuk
 • Shiga Ta Hanyar Tuwita
 • Shiga Ta Hanyar Gogul
 • Shiga Ta Hanyar Was'of
 • Adadin BaƘi 1673
 • Adadin Ra'ayoyi 0
 • -
  +

QARYA

Wednesday, May 18, 2016 6:57 AM

Matakin kamala na farko  

Kyakkyawan hali sharadi ne na rayuwar al'umma da kamalarta. Kyawun hali da dan adam tare su ka zo fagen samuwa dan haka shekarunsu daya. Babu wani da yake shakka game da muhimmancin kyakkywan hali da lizimtarsa domin lafiyar ruhin mutum da hutunsa da rabautarsa da sa'adarsa. Har ila yau babu wani mai inkarin tasirinsa mai amfani wajen qarfafawa da shiryar da tunanin al'umma wajen kawo gyara na gaba daya. Wane ne wanda yake jin zafin gaskiya da amana kuma yake neman sa'ada a cikin ha'inci da qarya? Ya isa hujja dangane da matsayin kyawawan hali cewa hatta al'ummar da ba ta yi imani da addini ba, tana yi wa kyakkyawan hali ganin girma da arziqi, kuma tana ganin cewa lalle ne ta bi salsalar hukumce-hukumcen kyawawan halaye a marhalolin wannan rayuwa.

A duk tsawon rayuwar mutum, duk da bambance-bambancen da ake da su wajen za6in hanyoyin rayuwa, kyawun hali ya kasance yana da asasi da tsari wanda kamanninsa suka yi daidai da na ko'ina a kowace al'umma.

Samuel Smiles mashhurin masanin nan na Biritaniya yace: "kyawawan halaye 6angare daya ne na qarfin da ke motsa wannan duniya. Kyawawan halaye a mafifitan kamanninsu sune ginanniyar dabi'ar 'yan adamtaka a mafificiyar surarta. Dan haka kyawawan halaye surar 'yan adamtaka ce ta haqiqa. Wadanda suka daukaka a wani 6angare na rayuwa suna qoqarin su jawo hankalin mutane zuwa gare su tare da dukkan girmamawa da mutuntawa, sannu a hankali sauran mutane za su amince da su har ma su yi koyi da su ta fuskar kamalarsu, saboda su na ganin cewa a wannan rayuwa kowane kyakkyawan abu ya ta'allaqa da su ne. Ba dan samun irin wadannan mutane a rayuwa ba, to da bai dace a zauna a rayu ba. Idan har sifofi da kamannin da aka gada kan ja hankalin mutane da yabawarsu to lalle kyawawan halaye su na wajabtawa a girmama kuma a mutunta ma'abocinsu. Kamanni da sifofi wasu abubuwa ne da ake gadon su a halitta, amma kyautata halaye kuwa sakamakon aiki da hankali ne da dagewa tuquru, hankali kuwa yadda kowa ya sani shine yake hukumta mu yake gudanar da al'amuranmu duk tsawon rayuwar mu. Wadanda suka kai qololuwar martaba da girma kamar fitila ce babba a kan hanyoyin rayuwar dan adam, suna haska duniya suna shiryar da mutane ga tafarkin mutumtaka da taqawa. Idan mutane ba su kintsu a halayyarsu ba, a kowace al'umma suke kuwa, to ba za su daukaka ba ko da wane irin haqqin siyasa da 'yanci a ka ba su. Ba larura ba ne ga wata al'umma dan kawai tana da faffadar qasa ta zama tana da daukaka da mutunci, al'umma tana iya zamowa mai yawan jama'a da kuma yalwar qasa amma kuma ta rasa dukkan sharudan kamala da daraja, matuqar halayen qwarai suka gurvace a al'umma to da sannu za ta halaka."

Abin da wannan masani na qasar Ingila yake fada dukkan mutane sun yi ittifaqi a kansa, amma mutane suna bambanta tsakanin ilmi da aiki, suna sanya sha'awance-sha'awancen su irin na dabbobi a matsayin aiki maimakon su sanya halayensu na qwarai.

Da'iman suna neman abubuwan sha'awa masu rudi wadanda suka bayyana a rayuwa kamar yadda kumfa kan bayyana a kan ruwa. Mutum ya shigo fagen rayuwa ne dauke da buqatun zuciyarsa wadanda suke kishiyoyin juna ne. Shi fagen gwabza yaqi ne a zatinsa tsakanin sifofin alheri da na sharri. Matakin farko na sifantuwa da 'yan adamtaka da kuma tsarkaka daga sifofin sharri, shine ya hadiye fushinsa ya kame sha'awarsa a wannan fagen fama. Domin su biyun nan sune matsirar halayen dabbanci.

Wajibi ne a kan wanda yake son kamala ya nisanci zurfafawa a cikin su. Har ila yau kuma ya musanya sha'awowinsa masu tsirowa daga gare su har su zamo kyawawa masu amfani. Mutum zai iya amfana qwarai daga irin abubuwan da yake jin su a zuciyarsa amma abubuwan da za su zama na alheri kawai su ne wadanda ke biyayya ga umarnin hankali.

Wani masani yana cewa: "Abubuwan da mutum yake ji a zuciyarsa kamar taska ce wadda ta kasu kashi biyu, 6angare daya daga cikinsu shine tsanani, dayan kuma gwagwarmaya, a kan na tsanani to zai iya hukumta kansa kamar yadda ya so ba kamar yadda ransa din ya so ba."

Wadanda suka daidaita qarfin zukatansu da na sha'awance-sha'awancensu da kuma abubuwan da mafarkinsu yake raya musu, har ila yau kuma suka shirya tsakanin zukatansu da hankulansu, to babu shakka sun kamo hanyar sa'ada a tsakanin mishkilolin rayuwa nesa da rauni da tozarta da faduwa.

Gaskiya ne cewa a yau qwarewa ta canza ta kai ga ci gaba da qaruwa da ha6aka da harka da gaggawa kamar qarfin wutar lantarki, alal misali. Mutum kuwa a yau saboda qwazonsa da qarfin kwanyarsa ya kai ga qarqashin Teku amma, abin tsiya da canje-canjen da muke gani tsakanin wannan ci gaba suna dorewa suna sanya mutane a cikin guguwar mishkiloli da masifu da tamolar 6ata da sakana, duk wannan abu ba abin da ya jawo su in banda fandarewa daga sahihin tafarkin kyawawan halaye da tsarkake ruhi.

Dakta Jawel na qasar Rum yace: "Ba shakka ilmi kam ya ci gaba a wannan zamani amma tun a marhalar farko kyawawan halaye da buqatun zuciya suka dakata, idan da su suna ci gaba da gudunmuwarsu tare da hankali da tunani kafada da kafada to da zai yiwu mu yi batun ci gaban mutum da kuma 'yan adamtaka."

Duk wani ci gaba da bai ba wa hukumce-hukumcen kyawawan hali hanyar gudana ba to kamar yadda yake a qa'idar adalci babu abin da ya saura gare shi illa halaka da lalacewa. Aukuwar bala'i iri-iri da tawaya a cikin al'ummar yau na bayyana buqatar mutane a sarari ga jiga-jigan halayen qwarai. Sune za su iya farfado da ruhi da rayuwa a jikin wannan matacciyar wayewa kuma su ba ta qarko.

Illolin Qarya

Kamar yadda gaskiya take da kyau da fa'idoji, haka nan qarya take da muni da illoli. Gaskiya tana daga cikin sifofi mafiya kyau, qarya kuwa tana daga mafiya muninsu. Harshe shine kakakin zuciya mai fassara abin da mutum yake yi cikin zuciyarsa. Idan hassada da qiyayya suka jawo yin qarya, to ta kan haifar da fushi mai tsanani kuma mai hatsari, idan qwadayi ko sabo-da-yi ne suka haifar da ita, ta kan jawo sha'awa mai ruruwa a zuciyar mutum. Idan qarya ta yi kanta ko tsatsa a harshen mutum har daudarta tayi annakiya a jikinsa, to za ta yi awon gaba da mutuncinsa, kamar yadda guguwa take kwashe ganyen bishiya.

Qarya tana damfara daudar ha'inci a zuciyar mutum ta dushe hasken ruhinsa. Har ila yau kuma tana wargaza hadin kai da amincewa da juna ta haifar da munafunci a al'umma. Yawancin 6ata, zaqin baki da shaci-faxi marar tushe da ake yi dan jawo wa kai amfani, su suke jawo shi.

Ma'abota mugun nufi yawanci su kan kai ga cim ma munanan manufofinsu ne ta hanyar lullu6e gaskiya da zaqin baki da magana mai dadi ta yaudara, har su samu su rinjayi mutane masu sauqin kai.

Maqaryaci ba ya dakatawa ya yi la'akari da tunani, sam ba ya yin tunanin game da qarshen al'amarinsa saboda yana riya cewa babu wani wanda zai san sirrinsa har abada. A maganganunsa akwai yawan kuskure da tubkar makaho, da sannu kuwa asirinsa zai tonu ya karye ya 6al6ace ya kunyata. Dan haka fadin da ake yi cewa, maqaryaci ya cika mantuwa, gaskiya ne.

Daya daga cikin dalilan da ke jawo yin qarya shi ne fadin da ake yi cewa: "Qarya mai kawo gyara ta fi gaskiya mai kawo 6arna." Wannan batu ya zama mafaka ga masu aikata wannan mummunan hali.

Sau da yawa mutane sun dogara da irin wannan batu wajen halatta qaryarsu. Alhali sun gafala daga qaidin da hankali da shari'a suka kallafa wa wannan halalcin. Sharadin da shari'a da hankali suka gindaya shine, idan jini ko mutunci ko tarin dukiyar mutum zai halaka to ya wajaba a kare shi ko ta halin qaqa, ko da ta hanyar yin qarya ne kuwa, domin larura ne. Larura kuwa tana gusar da uziri, amma fa duk da haka daidai ruwa daidai gari, bai halatta ba a shara qaryar da za ta wuce gwargwadon larura ba. Idan kuwa har muka fadada da'irar wannan larurar dan amfanin kanmu da son ranmu, kuma muka yi qoqarin fakewa da wannan qa'ida a kowane amfani da son rai, to babu wata qarya kenan da za ta zama ba ta da amfani.

Wani daga cikin manyan marubuta yace: "Kowane abu yana da musabbabi, kuma za mu iya qagawa kowane aiki musabbabi, mujirimai fandararru ma za su iya sama wa zaluncinsu uzurori da madogara.

Saboda haka kowace qarya da ake yi a duniya tana da amfaninta da fa'idarta, wato kowace qarya tana da 6angaren alheri da amfani, idan ba ta zama haka ba kuwa to lagawu ce da wasa, idan kuwa ta zamo hakan to babu cutarwa mai yawa a cikin ta. Hakan kuwa shine ta yadda dabi'ar mutum za ta sa shi ya iya daukar duk abin da ya dace da alheri da amfanin kansa. Idan ya ga amfaninsa da shi kansa za su shiga hatsari saboda gaskiya, ko ya tsammaci alheri a yin qarya sai ya yi qaryar ba wata-wata.

Domin ya hango fitina da sharri a cikin gaskiya, ya gano alheri da fa'ida kuma a cikin qarya." 'yancin magana ya fi 'yancin tunani muhimmanci, domin idan a ka sami illa a tunani, shi ma'abocin tunanin kawai za ta cutar, alhali 'yancin magana yana shafar al'umma ne baki daya, haka amfaninsa da illarsa duka al'umma za su shafa.

Gazzali yace: "Harshe yana daya daga cikin manyan ni'imomi. Duk da cewa shi ga6a ce qarama tattausa amma ta fuskar da'a da 6arna ba qarami ba ne, domin ba a bayyana kafirci ko imani sai da harshe. Sune kuwa qololuwar ibada da sa6o."

Ya qara da cewa: "Wanda zai tsira daga sharrinsa kawai shi ne wanda ya kange shi da addini ba ya sakin shi sai ga abin da yake mai amfani ne ga addininsa da duniyarsa da lahirarsa.." Littafin Abu Hamid Gazzali mai suna Kimiyaye sa'adat

Lalle ne mu nesanci yin qarya da duk wani zance da ya sa6a wa haqiqa a gaban yara domin kada su dauki wannan mugun hali daga gare mu. Saboda su yara nan da nan za su koyi halayyar wadanda suke zaune da su musamman ma idan ana aikatawa akai akai.

Gida shine ajin tarbiyyar yara muddin kuwa maganar iyaye ta sa6a wa gaskiya to yara ba za su zama masu gaskiya da riqon amana ba. Moris T. Yash yace: "Fadin gaskiya da tunanin ta da dogewa a kan ta dabi'a ce kawai ga wanda aka tarbiyantar da shi a kan ta tun daga yaranta."

Matsayin qarya a Addini Alqur'ani mai tsarki ya qirga mai yawan qarya a cikin wadanda ba su yi imani ba. Wadanda ba su yi imani da ayoyin Allah ba sune suke qirqira qarya." (surar Nahli:105) Daga wannan aya za a fahimci cewa mumini ba ya dulmiya a cikin daudar qarya.

Manzon Allah (SAWA) yana cewa: "ku riqe gaskiya lalle gaskiya tana shiryarwa zuwa ga da'a, da'a kuma tana shiryarwa zuwa ga aljanna. Mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya kuma yana bin ta har sai an rubuta shi mai gaskiya a gurin Allah. Kuma lalle ku nisanci qarya domin qarya tana kaiwa ga fajirci, fajirci kuma yana kaiwa ga wuta, mutum ba zai gushe ba yana qarya har sai an rubuta shi qurgurmin maqaryaci a gurin Allah." Littafin Nahjul fasaha shafi na 418

Rashin gaskata abu sai da qyar da matsawa na daga dabi'un maqaryata dan haka ne Manzon Allah (SAWA) yake cewa: "wadanda suka fi gaskiya a magana sune suka fi gaskata mutane. Wadanda suka fi qaryata mutane kuwa sune suka fi qarya a magana." Littafin Nahjul fasaha shafi na 118

Dakta samuel smiles yace: "Wasu mutane sun xauki xabi'arsu ta qasqanci a matsayin ma'auni ga xabi'un sauran jama'a alhali kuwa mun san cewa alal haqiqa mutane madubi ne ga halayenmu. Duk abin da muka gani a jikinsu na sharri ko na alheri to ba wani abu ba ne illa hoton abin da ke cikin zuciyarmu."

Duk wanda ya kasance gwarzon ladubba da sadaukin halayen qwarai to qarya ba za ta ra6o kusa da shi ba. A zuciyar maqaryaci akwai wata cuta da take gigita shi ta hana shi tsai da magana.

Wanda yake jin rauni da qasqanci a cikin zuciyarsa shine yake gauraya maganar sa da qarya, domin qarya itace mafakar rarraunan mutum raggon maza mai tsoro, kamar yadda Imam Ali (AS) yake cewa: "Idan da za a warware abubuwa to da gaskiya ta kasance tare da jarumta, qarya kuma ta kasance tare da ragwantaka." Littafin Gurarul Hikam shafi na 605

Dakta Raymond Peach yace: "Qarya itace babban makamin kare kai ga raunana kuma itace mafi girman hanyar da za su goce wa hatsari. Dan haka ne yawanci qarya ba wata aba ba ce illa sakamakon gazawa da faduwa. Da za a tambayi yaro qarami cewa, ko kai ne ka gutsire 'yar alawar nan, ko kuma kai ka fasa wannan kaskon? Matuqar ya san in ya fadi gaskiya zai dandana kudarsa to dabi'ar kariya za ta sanar da shi yace a'a." Littafi Ma wa Farzandan e Ma

Imam Ali (AS) ya bayyana fa'idoji da ribar gaskiya kamar haka: "Mai gaskiya ya kan samu abu uku: kyakkyawar amincewa, soyayya da kuma kwarjini." Littafi Gurarul Hikam shafi na 605

Imam Sadiq (AS) ya bayyana cewa gaskiya itace mizanin salihanci ba yawan sallah da azumi ba. Inda yace; "Kada yin sallarsu da yin azuminsu su rude ku, domin wani ya kan yi sallah da azumi ne saboda in ya bar su zai kasance a cikin haso ko kaxaici, amma ku jarraba su da gaskiyar magana da kuma riqon amana." Littafin Usulul Kafi, juz'i na 1 shafi na 460

Imam Ali (AS) yana cewa: "Qarya itace mafi munin halaye." Littafi Gurarul Hikam shafi na 175

Dakta Samuel smiles yace: "Qarya tana daga cikin miyagun halaye da sifofi ababan zargi, lalle ne mutum ya dage ya ga cewa gaskiya da riqon amana sun zame masa wuqar gindi a kowane tudu da gangare na rayuwa, kada ya kuskura ya salwantar da su ko ta halin qaqa ko da na dan gajeren lokaci saboda wata buqata ko manufa." Littafin Akhlaq

Addinin musulunci ya dora gininsa na gyaran halayya bisa asasin imani, kuma ya sanya imanin ya zama asasin samun sa'adar mutum.

Deskarte yace: "kyawun hali ba tare da imani ba, ta gina ne kawai ba ta shiga ba." Wani masanin kuma yace: "Kyawun hali ba imani kamar shuka iri ne a Kanfa ko kuma a cikin qayoyi, kuma ru6ewa kawai zai yi ya mace. Mafifitan darajojin halayen qwarai idan ba daga addini suke ba to kamar gawa ce kawai a gaban mutum mai rai."

Addini shi ne alqalin hankali da zuciya don haka shi ne mai sulhunta tsakaninsu. Koyarwar addini tana rage dulmiyewa cikin abin duniya, kuma tana gindaya shamaki mai kariya tsakanin mutum da miyagun al'amura dabam-dabam. Wanda yake cike da imani da'iman yana bin wani maqasudi ne har wa yau kuma koyaushe a cikin nutsuwa yake.

"To da ambaton Allah zukata suke nutsuwa." (Surar Ra'adi: 28)

Musulunci ya sanya imani da halayyar mutunci a matsayin mizanin darajar mutum da kuma qoqarinsa na qarfafa wadannan madogarai guda biyu a zuciyarsa. Sai ya sanya imanin mutum a matsayin lamunin gaskata maganarsa tun daga yarda da rantsuwarsa a gurin shari'a da sharudan da suke matsayin dalili mai raba gardama, ya kuma sanya shaidarsa a matsayin daya daga cikin hanyoyin tabbatar haqqoqi.

Idan har qarya ta shigo cikin ba da shaida da tabbatar da haqqoqi to kuwa sanin kowa ne cewa za ta yi cutarwa da ba ta da iyaka. Dan haka ne aka qirga ta a cikin abubuwa da ba za a gafarta su ba. "Kuma kada ku kar6i shaidarsu har abada." (surar Nur :4)

Irin cutarwar da qarya take jawowa ta wadatar wajen tabbatar da girman zunubinta, amma yin qarya a gurin ba da shaida da rantsuwa ya fi cutarwa da 6arna dan haka zunubinsu yafi girma.

Qarya hanya ce ta fadawa cikin sauran miyagun halaye. Imam Hassan askari (AS) yana cewa: "An sanya dukkan miyagun halaye a cikin wani gida kuma aka sanya qarya mabuxinsa." Littafin Jami'us sa'adat, juz'i na 2, shafi na 218

Domin qara haske ga wannan hadisi ga wani hadisi na Manzon Allah (SAWA) da yake cewa: Wani mutum ya zo garin Manzon Allah (SAWA) ya roqe shi ya yi masa wa'azi, sai Manzon Allah (SAWA) yace masa: "ka daina yin qarya ka yi guzuri da gaskiya". Sai mutumin ya tafi. Sai ya kasance yana cewa shi a da mai yawan aikata zunubi ne amma dole ya bari. Domin idan aka tambaye shi in ya fadi gaskiya to zai kunyata kansa in ya yi qarya kuma ya sa6a wa Annabinsa. Da ya riqe abin da Manzon Allah (SAWA) ya gaya masa sai ya tsira daga zunubi ya tsarkake kansa.

Lalle duk wanda ya kasance tare da masu gaskiya kuma ya yi gaskiya a magana da aiki zai rayu nesa daga nadama da hasara. Zai zama mai lafiyayyen tunani, zuciyarsa kuma ta cika da imani babu qunci ba damuwa ya tsira daga rudun tunani. Mummunan qarshe da qarya ke jawowa a addini da lamarin duniya shi ne darasi mafi girma ga duk wanda ke son ya rayu cikin daukaka da mutunci da karama.

Qarshen al'amarin qarya tsumagiyar kan hanya ce. Ba a samun kamala sai a qarqashin inuwar halayen qwarai tare da imani, matuqar ba a samu wannan kamalar ba to babu yadda za a yi a samu sa'ada.

 

Mun kawo muku wannan maqala ne daga rubututtukan mashhurin malamin tarbiyya nan, Sidi Mujtaba Musawi Lari (Allah Ya yi masa rahma).

Illar qarya

Ra'ayoyin Masu Shigowa
Babu Haƙƙin Tasarrufi.
www.haditv.com | Powerd by : Dijlah