Tuwita
Fesbuk
Gogul
Yutob
Rss

Adalcin Sahabbai (1)

Adalcin Sahabbai (1)
 • Mr. Hassan Adamu
 • 2017-09-18 07:09
 • Fitarwa
 • PDF
 • Shiga Ta Hanyar Fesbuk
 • Shiga Ta Hanyar Tuwita
 • Shiga Ta Hanyar Gogul
 • Shiga Ta Hanyar Was'of
 • Adadin BaƘi 1577
 • Adadin Ra'ayoyi 0
 • -
  +

Adalcin Sahabbai

 

Wednesday, September 13, 2017

9:53 AM

 

Babu shakka cewa Sahabban Annabi (S.A.W.A.) suna da wasu falaloli ko fifiko da suka ke6anta dasu. Saboda Ayoyi da Wahayi daga bakin Annabi (S.A.W.A.) suka riqa ji, sun ga Mu'ijizojinshi, da maganganushi masu albarka suka sami tarbiyya sannan kuma sun amfana daga irin ayyukan shi abin koyi da kuma hanyar kyawawan Dabi'u shi.

Dan haka a cikin su akwai wadanda suka tarbiyantu, kuma suka sami matsayi babba wadda duniyar musulunci take taqama da tinqaho da samuwar su, amma batu muhimmi anan shine, shin dukkan Sahabbai ba tare da ware ko daya ba, sun kasance muminai, salihai, masu gaskiya, masu aikin qwarai kuma adilai ko kuma a cikin su akwai wadanda suke ba salihai ba?

Aqidu biyu masu kishiyantar juna

Dangane da sahabbai akwai aqidu biyu mabambanta: ta farko itace cewa, dukkan su ba tare da wariya ba wato cewa muminai ne, adilai ne, masu taqawa ne, masu gaskiya ne kuma salihai ne. A dalilin haka duk wanda a cikin su ya naqalto ruwaya daga Annabi (S.A.W.A.), daidai ce kuma abin kar6a ce, kuma ba za a ta6a yin ko 'yar shakka akai ba, kuma sannan idan aka ga sunyi wani aiki da ya sa6a, to dole ne a kare su akan wannan aiki, wato a nema musu mafita akan wannan aiki. Wannan itace aqidar 6angare mai girma daga ahlus-sunna.

Dayar aqidar kuma itace: Duk da yake a cikin su akwai manya masu matsayi, taqwa da tsoron Allah, sadaukarwa da kuma tsarkakakkar zuciya, to amma a cikin su ma akwai munafukai kuma maqaryata kamar yadda qur'ani mai tsarki da Ma'aikin Allah (S.A.W.A.) suka wofintar dasu.

Ta wata surar, wadannan sune ma'aunai da zamu riqa amfani dasu a ko'ina domin tantance mutane na gari daga wasunsu, kuma dole muyi aiki dangane dasu, amma saboda su sahabban Annabi (S.A.W.A.) ne, a asali zamu yi musu kallo mai kyau ne, amma kuma ba zamu ta6a rufe idanun mu daga gaskiya ba sannan ba zamu dauke idanun mu daga gangarowar ayyukan da basu dace ba daga gurin su, kamar rashin adalci, munafinci ko qarya d.s., saboda yin hakan wato zai kasance illa da cin zarafin shi addinin ne da kuma musulmai, kuma zai jawo nutsewar munafukai cikin harabar musulunci.

'yan shi'a da kuma wasu masu kyakkyawar fahimta daga cikin ahlus-sunna sun yarda da wannan aqidar.

Masu wuce iyaka wajen tsarkake wasu

Wasu gungu daga cikin masu tsarkake sahabbai sun kai haddin da  suna ganin duk wani mai bayyana nazarin shi dangane da ayyuakan wasu sahabban, a matsayin fasiqi, kafiri, mushriki ko zindiqi kai har ma suna ganin jinin shi ya halatta!!

 

Kamar yadda zamu iya gani a littafin «الاصابة»  na Abu Zar'atu Ra'zi yana cewa: Duk lokacin da kaga wani yana sukan Sahabbai, ka sani cewa shi zindiqi ne, kuma saboda cewa Ma'aikin Allah (S.A.W.A.) gaskiya ne da kuma qur'ani gaskiya ne, da abin da yazo dashi gaskiya ne sannan duk wadannan abubuwa sahabbai ne suka kawo mana su, dan haka suna (maqiya) so su wawantar mana da tunanin mu ne dan mu rasa littafi da sunna.[1]

 

Abdullah Musala a littafin shi mai suna «حتى لا ننخدع»  yana cewa: Su (wato sahabbai) abokan zama ne wadanda Allah Ya za6awa AnnabinShi, wadda Ya zae shi domin tabbatar da addini da shari'arShi kuma Ya za6a mashi su a matsayin waziranshi, dan haka son su shine addini da imani kuma qin su kafirici ne da munafunci! Kuma Ya wajabtawa al'umma son su da kuma kodayaushe su riqa ambaton alkhairan su da falalolin su, kuma al'umma suyi shiru akan sa6ani da yaqoqin da ya faru a tsakanin su!.[2]

 Alhalin zamu gani cewa wannan maganar ta sa6awa littafi da sunna.

Tambayoyin da basu da amsa

 

A nan duk mai hankali da sanin yakamata wanda ba zai ta6a kar6ar maganganun da babu dalili ba, zai tambayi kanshi wadannan tambayoyin:

 

Allah (T) a cikin Al'qur'ani mai tsarki dangane da matan Annabi (S.A.W.A.) Yana cewa:

 

 

يَانِسَاءَ النَّبىِ‏ِّ مَن يَأْتِ مِنكُنَّ بِفَحِشَةٍ مُّبَيِّنَةٍ يُضَعَفْ لَهَا الْعَذَابُ ضِعْفَينْ‏ِ  وَ كاَنَ ذَالِكَ عَلىَ اللَّهِ يَسِيرًا

 

Yã mãtan Annabi! Wadda ta zo da alfãsha bayyananna daga cikinku zã a ninka mata azãba ninki biyu. Kuma wancan yã kasance mai sauƙi ga Allah.[3]

 

Dan haka duk irin fassarar da zamu yiwa ma'anar  sahabbai (wadda tafsirai iri-iri akan haka na nan zuwa) babu shakka matan Annabi (S.A.W.A.) sune mafi bayyanuwar su, to gashi mun gani qur'ani mai tsarki yana cewa ba wai kawai ma baza a hukumtasu akan laifin su ba idan sunyi, har ma za a ru6anya musu horo ne.

 

Shin zamu yarda da aya ne ko kuma maganganun masu qumazin tsarkake sahabbai ba tare da qaidi ko sharadi ba?

Hakazalika dangane da kurakuran dan Nuhu (AS) qur'ani mai tsarki yana gaya mana:

«إنه عمل غير صالح»  wato shi aiki ne ba mai kyau ba[4] kuma har horon Nuhu akayi cewa kada ya nemar mashi gafara!

To shin dan Annabi yafi muhimmanci ko kuma sahabban shi?

Haka ma akan matar Nuhu (AS) da matar Lut' (AS) (manyan Annabawan Allah ne) qur'ani yana gaya mana:

... فَخَانَتَاهُمَا فَلَمْ يُغْنِيَا عَنهْمَا مِنَ اللَّهِ شَيْا وَ قِيلَ ادْخُلَا النَّارَ مَعَ الدَّاخِلِين

saisuka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga.[5]‏

shin wadannan ayoyin qur'anin ba suna gaya mana a fili cewa ba: ma'aunin (yadda ake gane) mutanen kirki da na banza shine imanin su da ayyukan su ba, kuma hatta kasantuwar su mata ko dan Annabi, munanan ayyukan su basu hana a tausa su a wuta ba?

Duk da wannan shin ya dace mu rufe idanun mu muce tunda wane ya kasance ne, son shi ya zama addini da imani kuma qin shi kafirci da munafunci ne? Ko da kuwa daga baya ya kasance cikin munafukai kuma ya cutar da zuciyar Annabi (S.A.W.A.) ko kuma ya ha'inci musulmai?

Shin hankali da tunani zai yarda da wannan maganar?

Idan mutun yace, Talha da Zubair a farko sun kasance mutanen kirki, to amma me zaka ce a lokacin da son mulki ya shige su, suka tafi tare da matar Annabi (A'isha) suka katse alqawari da bai'ar su daga Imam Ali (AS) wadda mafi rinjayen al'ummar musulmi suka yiwa bai'a, kuma suka kunna wutar yaqin Jamal da yayi sanadiyar mutuwar musulmai kusan dubu 17 a fitinar da suka kunna, suka kauce daga hanya madaidaiciya kuma jinin waannan dubunnan mutane yana wuyansu, to a ranar gobe qiyama wane jawabi zasu bayar.

Shin wannan maganar (maganar cewa dukkan su adilai ne) ba tayi nesa da haqiqa ba?!

Ko kuma idan mutun yace mu'awiyya azzalumi ne a sakamakon karya bai'ar Imam Ali (AS) da yayi da kuma rashin yarda da haqqin da gungun musulmai da daidaikunsu suka yarda dashi, da kuma a sakamakon kunna wutar yaqin Siffin da yayi wadda ya jawo zubar da jinin musulmai sama da dubu 100, dangane da duk wadannan ayyukan mu'awiyya, idan aka ce azzalumi ne shi qarya aka fada?!

Shin za a iya rufe idanu daga wadannan abubuwan tarihi mai daci ko kuma  qoqarin canja su za ayi da yin kwaskwarima - abin da duk wani mai hankali ba zai yarda da shi ba- ga duk wadannan aika-aika masu matuqar muni da suka faru?! Shin son irin wadannan mutanen ne – kamar yadda Abduullah Mausul yace– imani da addini ne kuma qin su munafunci da kafirci ne?! shin muna da damar muyi shiru dangane ayyukan ta6argazar da suka jawo salwantar dubunnan rayuka?! Wanne hankali ne zai hukumta haka? Qur'ani yana cewa a gefen Annabi (S.A.W.A.) akwai wadanda suke munafukai ne su, shin duk sai mu rufe idanu daga duk wadannan ayoyin?

Qur'ani yana cewa:

وَ مِمَّنْ حَوْلَكمُ مِّنَ الْأَعْرَابِ مُنَافِقُونَ  وَ مِنْ أَهْلِ الْمَدِينَةِ  مَرَدُواْ عَلىَ النِّفَاقِ لَا تَعْلَمُهُمْ  نحَنُ نَعْلَمُهُم...

Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai, haka kuma daga mutãnen Madina. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su‏

Shin muna tunanin duniyar hankali zata kari wadancan maganganu (wato kau da kai daga dukkan su ko kuma yi musu kudin goro)?!

Su waye Sahabbai?

Wani batu muhimmi a nan shine me ake nufi da Sahabi.

Dangane da cewa wadanne sahabban ne irin wannan tsarkakewar ta nisanta dasu, akwai ta'arifofi ko ma'anoni mabambanta da suka zo daga malaman ahlus-sunna.

Wasu suna cewa ne duk wanda daga musulmai yaga Annabi (S.A.W.A.), to yana cikin sahabban shi! Daga cikin wadanda suka ambaci haka akwai Bukhari yana cewa:

من صحب رسول الله (صل الله عليه و سلم) أو رآه من المسلمين فهو من أصحابه!.

Ahmad bin Hambali fitaccen malamin ahlus-sunna shima yana cewa:

أصحاب رسول الله (صل الله عليه و سلم) كل من صحبه شهرا أو يوما أو ساعة أو رآه.

Sahabin Annabi (SAW) shine duk wanda ya lizimce shi wata daya ko kwana daya ko awa daya, ko kuma ya ganshi!.

Wasu kuma sun dauki ma'ana tsukakkiya ne ga ma'anar sahabi, misali qadhi abubakar muhammad bin al-Tayyib yana cewa:

duk da yake ma'anar sahabi a lugga faffada ce (wato tana da fadi), amma a al'adar mutane wannan kalmar ana ke6anta tane kadai ga  wanda ya zauna ko ya rayu da Annabi (SAW) na wani lokaci da za a iya cewa eh, sun rayu tare na wasu lokuta, ba wai ga wanda kawai awa daya ya zauna dashi ba, ko kuma dan yayi xdn tattaki tare dashi, ko kuma wanda ya ruwaito hadisi guda daya daga gare shi ba.

Wasu kuma kamar Sa'id bin Al-musayyib sai ya dan dada matse hannu wajen ma'anar inda yake cewa: Sahabban Annabi (SAW) sune kadai wandanda suka halarci yaqi daya ko biyu tare da Annabi (SAW) a mafi qarancin shekara daya ko biyu.[6]

A taqaice wadannan ta'arifofin ko ma'anonin da kuma wasun su wadanda bamu ambato ba saboda gudun tsawaita magana, yana nuna cewa ba a san haqiqanin wadanda waccan tsarkakewa ta qunsa ba, amma mafi yawan mutune sun auki faffadar ma'anar ne,  duk da yake akan abun da muke so muyi magana hakan ba zai kawo mana wani canji na azo a gani ba, saboda da yawa daga cikin guraren ja-in-ja din wadda za ayi bahasin su nan gaba,  sune wadannan din dai da suka rayu da Annabi (S.A.W.A.) lokaci mai tsawo.

Abu na asali da ya samar da aqidar tsarkakewa

Duk da yake cewa aqidar tsarkake sahabbai wadda ta wata fuska tana yin kama da Isma' (wato tsarkakewa ta haqiqa daga dukkan kurakurai), babu ita a qur'ani kuma babu ita a sunna, saidai ma suna (qur'ani da sunna) inkarin ta ne (wato aqidar tsarkakewar), kai ance ma a qarni na farko babu wannan aqidar kwata-kwata, dan haka ya kamata mu gano cewa menene dalilin da yasa wannan mas'ala ko batu ya bijiro a qarnuqan baya.

Samuwar wannan aqida bai zai rasa dalilai kamar haka ba:

Mafi kyawun zaton akan hakan shine kamar yadda yazo a wasu bahasosin da suka gabata, wasu suna cewa idan sahabbai suka rasa cikakkar tsarkakewa, to sarqar dake tsakanin su da Annabi (S.A.W.A.) zata tsinke ne, saboda littafin Allah da kuma sunnar Annabi (S.A.W.A.) ta hanyar su suka iso gare mu.

Amma amsar wannan maganar a bayyane take, saboda babu wanda dama ya tafi akan cewa dukkan sahabai maqaryata ne ko ba daidai suke ba, dan me! tabbas a cikin su akwai wadanda suke amintattu masu yawan gaske kuma su wadannan din zasu iya kasancewa sarqar da zata hada mu da Annabi (S.A.W.A.),  kamar yadda muke fadar hakan ga mataimakan (sahabban) Ahlul-baiti (AS).

Wani abin jan hankali shine a qarnukan baya ma akwai wannan matsalar, saboda muma ta hanyar wasu ne muke tuqewa ga zamanin Annabi (S.A.W.A.), amma kuma babu wanda yake cewa dukkan wadannan hanyoyin ingatattu kuma dukkan su tsarkaka ne kuma idan ba haka ba, addinin mu zai gushe.

Hasali ma kowa yana cewa ne dole a riqa kar6ar ruwayoyi daga mutanen da suke adilai ne, littattafan Rijal saboda haka akayi su wato tantance adilai amintattu daga wasun su, to yanzu mai zai hana dangane da sahabbai muyi aiki kamar yadda mukeyi a dangantakar mu da sauran mutane?!

Tunanin cewa fadin aibun wasu daga cikin sahabbai, wai zai rage qimar Annabi (S.A.W.A.) ne, dan haka bai halatta ba.

Ya kamata mu tambayi masu irin wannan tunanin cewa: Ashe qur'ani ba yayi bulala (qalubalanta) ga munafukan da suke a kewaye da Annabi ba?! Shin kasantuwar su a cikin sahabban Annabi (S.A.W.A.) nagartattu masu imani na haqiqa, ya rage wani abu daga qimar shi ne? Ko kaan haka ba zai ta6a yiwuwa ba!

A taqaice, kullum kuma a kowanne zamani, hatta a zamanin dukkan manyan Annabawa (AS), akwai mutane na gari da kuma 6ata gari kuma ba zasu iya cutar da matsayin su ba ko kadan.

Duk lokacin da batun binciken ayyukan sahabbai ya taso, yana komawa ga al'amuran da suka faru na khalifofin farko ne, saboda haka domin kare mutuncin su dole ne a qarfafa akan batun tsarkake su, dan kada wani ya sa alamar tambaya ga ayyuka irin na zamanin Usman dangane da baitul-mali da makamantansu da suka faru,  kuma kar ya soki khalifa yace me yasa akayi kaza da kaza!

Hatta mu'awiyya da ayyukan shi kamar adawa da yaqar shugaban musulmai (Ali A.S.) da kuma kunna wutar yaqin da ya lashe rayukan dubunnan musulmai da zubar da jinin su, zai iya yin duk wannan kwaskwarimar domin ya nisanta kanshi daga masu suka ko binciken irin wadannan munanan ayyuka da suka faru.

Saidai duk da yake gaskiyar magana itace wannan aqidar tsarkakewa ko wanke sahabbai ta samo asali ne daga 'yan siyasar qarnonin farko, kamar yadda tafsirin ayar «أولوا الأمر»  ya qunshi har da hakiman ko sarakunan kowanne zamani – wai a faffadar ma'anar kalmar – wadda ta hada har ma da azzaluman sarakunan bani abbas da bani umayya, duk wannan ma shirin 'yan siyasar sarakunan ne, kuma bana tunanin sakamakon wannan maganar ne ya zama mashigar halayen magoya bayan tsarkake dukkan sahabbai.

 Wasu kuma daban suna da aqidar, yarda da tsarkin sahabbai sakamakon umarnin wasu daga cikin ayoyin qur'ani da hadisan Annabi (S.A.W.A.) da suka zo dashi.

A zahiri wannan itace kwaskwarima ko wankiya mai dan dama-dama, amma itama a yayin da muka sa ta akan sikeli, za a samu cewa ayoyi da ruwayoyin da suke yin riqo dasu akan hakan, ba zasu samu abin da suke so daga cikin su ba.

Muhimmiyar ayar da suka yi riqo da ita a wannan batun ita ce:

وَ السَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَ الْأَنصَارِ وَ الَّذِينَ اتَّبَعُوهُم بِإِحْسَانٍ رَّضىِ‏َ اللَّهُ عَنهْمْ وَ رَضُواْ عَنْهُ وَ أَعَدَّ لهَمْ جَنَّاتٍ تَجْرِى تحَْتَهَا الْأَنْهَرُ خَلِدِينَ فِيهَا أَبَدًا  ذَالِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيم

Kuma mãsu tsẽrẽwa (magabata) na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; Ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.[7]‏

Da yawa daga cikin masu tafsirin ahlus-sunna a qarqashin wannan ayar suna kawo wani hadisi ne wadda (daga wasu sahabbai, daga Annabi) suka naqalto, abin da hadisi yake cewa:

جميع أصحاب رسول الله فى الجنة محسنهم و مسيئهم

Wato dukkan sahabban Annabi suna aljanna nagarin su da wadanda ba nagarinsu ba.[8]

Abin ban sha'awa dangane da abin da wannan ayar take magana shine, Tabi'ai zasu sami tsira ne a yayin da suka biyewa sahabbai a ayyukan qwarai (alkhairi) ba wai a munanan ayyuka ba, kuma wai ma'anar ta shine tana yiwa sahabbai tabbaci da alqawari da aljanna ne, to shin ma'anar wannan maganar, shine kasantuwar su 'yantattu akan zunubai wato su duk kurakurai da sa6on da za suyi ba komai?!

Shin kuna ganin Annabin da yazo domin shiryarwa da gyara al'umma, zai yiwu ace ya ke6e sahabbanshi a ayyuka, yace su ko menene suka yi babu komai?! Alhali qur'ani dangane da matan shi wadanda suna daga cikin mafiya kusancin sahabban shi, yana cewa: idan kuka yi sa6o horon ku zai kasance ninki wato zai ru6anya.[9]

Abin la'akarin shine koma wanne irin sarkakaqiya keda akwai a wannan ayar, to aya ta 29 ta surar Fat'h tana warware wannan sarqaqiya, domin tana bayyana sifar sahabban Annabi (S.A.W.A.) na haqiqa kamar haka:

... أَشِدَّاءُ عَلىَ الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنهَمْ  تَرَئهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ اللَّهِ وَ رِضْوَانًا  سِيمَاهُمْ فىِ وُجُوهِهِم مِّنْ أَثَرِ السُّجُود...

...Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda...

Shin zai yiwu ace waannan sifofi guda bakwai na wadanda suka kunna wutar yaqin Jamal da Siffin ne, kuma suka yiwa Imamin zamanin su bore, kuma suka kashe dubban musulmai? Shin haka sun kasance masu rahma a tsakanin su kenan?

Shin tsananin nasu akan kafirai ne ko kuma akan musulmai?!

 

[1] Al-Isabatu, mujalladi na 1, shafi na 17.

[2] Hatta la nankhadi'u, shafi na 2.

[3] Surar ahzab, aya ta 30.

[4] Surar Hud, aya ta 46

[5] Surar Tahrim, aya ta 10

[6] Tafsirin qurdabi, mujalladi na 8, shafi na 237

[7] Surar Tawba , aya ta 100.

[8] Tafsirin kabir, na fakhri razi da tafsir al-manar, qarqashin ita wannan aya ta 100 ta cikin surar tawba.

[9] Surar ahzab, aya ta 30.

Adalcin Sahabbai waye sahabi

Ra'ayoyin Masu Shigowa
Babu Haƙƙin Tasarrufi.
www.haditv.com | Powerd by : Dijlah