Tuwita
Fesbuk
Gogul
Yutob
Rss
  • Abul Hassan Ali bin Musa Ar-Ridha (AS) yana cewa: Tabbas a qasar Khorasan akwai wata Baq’ah wacce a wani lokaci za ta kasance muhallin kaiwa da komowar Mala’iku, wani mala’ika ba zai gushe yana sauka daga sama wani kuma yana hawa zuwa sama, har zuwa lokacin da za a busa Qaho. Sai suka tambaye shi, suka ce ya Dan Ma’aikin Allah wacce Baq’ah ce wannan kake Magana akai, sai yace: Ita wannan Baq’ah tana qasar Tusi, kuma na rantse da Allah wannan dausayi ce daga dausayoyin Aljanna, duk wanda ya ziyarce ni a wannan guri, ladanshi kamar na wanda ya ziyarci Ma’aikin Allah (SAWA) ne, kuma Allah (SWT) Zai bashi ladan Hajji sahihiya dubu da kar6a66iyar Umrah, kuma ni da Mahaifina za mu kasance masu cetonshi ranar Qiyama. – Amali sheikh Suduq.
  • 2016-08-13 10:08 PM

Babu Haƙƙin Tasarrufi.
www.haditv.com | Powerd by : Dijlah